Kisan Nuseirat : Iran Ta Caccaki Shirun Kasashen Duniya Kan Laifukan Isra’ila A Gaza

Iran, ta caccaki shirin kasashen Duniya akan munanen kisan da Isra’ila ke ci gaba da aikatawa a Gaza, musamman na baya baya nan a sansanin

Iran, ta caccaki shirin kasashen Duniya akan munanen kisan da Isra’ila ke ci gaba da aikatawa a Gaza, musamman na baya baya nan a sansanin Nuseirat, wanda a yayinsa Isra’ila ta kasha mutum sama da 200 jiya Asabar.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kan’ani ya yi Allah wadai da mummunan laifin da gwamnatin Isra’ila ta aikata a sansanin na al-Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar, Kan’ani ya ce kisan kiyashin da Isra’ila ta yi wa daruruwan Falasdinawa, musamman mata da kananan yara a sansanin al-Nuseirat, ya samo asali ne sakamakon gazawar da kasashen duniya suka yi wajen tunkarar zaluncin da gwamnatin kasar ta yi a Gaza cikin watanni 8 da suka gabata.

Ya kara da cewa kungiyoyin duniya, musamman ma kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, sun kasa daukar wani mataki na tunkarar laifukan yaki da gwamnatin Isra’ila ke yi da kuma keta dokokin kasa da kasa da na jin kai a zirin Gaza.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: “Ci gaba da aikata wannan laifin, ba komai ba ne illa karfafa masu da ake kan kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa.”

Ya yi kakkausar suka ga kasashen Turai da Amurka kan yadda suke ba wa Isra’ila da bama-bamai da makamai masu linzami.

Ya yi nuni da cewa, duniya ta shaida irin gazawar kungiyoyin kasa da kasa wajen kare al’ummar Falastinu, musamman mata da kananan yara.

A cikin wannan mummunan yanayi, in ji shi, kasashen musulmi wajibi ne su tashi tsaye wajen tinkarar hare-haren wuce gona da iri na Isra’ila, da kuma sauke nauyin da ke kansu na kare Musulunci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments