Kawancen Amurka Da Birtaniya Sun Sake Kai Wa Yemen Hari Ta Sama

Dakarun Amurka da na Birtaniyya sun kai wasu jerin hare-hare ta sama a sassa daban-daban na kasar Yemen a cikin daren jiya a wani mataki

Dakarun Amurka da na Birtaniyya sun kai wasu jerin hare-hare ta sama a sassa daban-daban na kasar Yemen a cikin daren jiya a wani mataki da suke cewa na karya karfin soji na kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ‘yan Houthi, dake kai hare-hare kan jiragen ruwa dake da alaka da Isra’ila domin nuna fishi kan yakin da Isra’ila ke yi a Gaza.

An kai wadannan hare-hare na hadin gwiwa ne kan wuraren Houthi 13 domin hana kai hare-hare a nan gaba, in ji rundunar sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya (Centcom).

“Dakarun Burtaniya sun shiga wani farmakin hadin gwiwa da sojojin Amurka da nufin dakile karfin soji na ‘yan Houthis da ke ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa na kasa da kasa a tekun Bahar Maliya da Tekun Aden,” a cewar wata ‘yar takaitacciyar sanarwar manema labarai.

A cewar sanarwar, bayanan sirri sun “tabbatar da” cewa wurare biyu a cikin Hodeida suna da hannu wajen kai hare-hare kan zirga-zirgar jiragen ruwa, da wuraren jirage marasa matuka da wuraren adana na’urori.

An kai hare-hare ta sama a yankuna daban-daban na kasar Yemen, ciki har da babban birnin kasar Sanaa, a daren Juma’a a cewar shaidu da kafofin yada labaran Yemen.

Tashar al-Masira da ke karkashin ikon ‘yan Houthi, ta ba da rahoton mace-mace da jikkata a wadannan hare-hare da ta danganta ga sojojin Amurka da aka tura yankin.

Tunda farko dai ‘Yan Houthi na Yamen din sun sha alwashin ci gaba da kai hare-hare cikin azama don goyon bayan Falasdinawa a yakin da Isra’ila ke yi a Gaza, kamar yadda shugaban kungiyar Abdulmalik al-Houthi ya fada a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments