Katafaren Jiragen Ruwa biyu Sun Yi Karo Da Nakiyoyi A Hurmuz

Majiyar dakarun IRGC a nan Iran ta bayyana cewa manya manyan jiragen ruwa biyu dauke da ganga miliyon 4.5 sun kama da wuta bayan sun

Majiyar dakarun IRGC a nan Iran ta bayyana cewa manya manyan jiragen ruwa biyu dauke da ganga miliyon 4.5 sun kama da wuta bayan sun yi karo na nakiyar sojojin ruwa a kudancin mashigar ruwa ta Hurmuz a yau Asabar, a lokacinda suke kokarin sake hanyar wucewa ta mashigar.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar na cewa, bayan da jaragen suka yi karo da nakiya suka kuma kama da wuta suka tsaya cik, matuka jiragen sun gudu sun bar jiragen suna konewa.

Labarin ya kara da cewa, sojojin Amurka da ke yankin ne suke kodaitar da jiragen satar hanya wucewa daga kudancin mashigar Ruwan ta Hurmuz, sannan a duk lokacinda irin haka ya faru ba zaka ji duriyarsu ba.

Amurka da kasashen yammam suna son ganin sun bude mashigar ruwa ta Hurmuz ko ta kaka, saboda fitar da kansu daga matsalolin da suka jefa kansu bayan farwa kasar Iran da yaki. Na karancin makamshi da wasu bukatun da suke samu daga kasashen yankin tekun farisa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted