Kasuwanci Tsakanin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Da Kasashen Nahiyar Afirka Ya Kai Dala Biliya 1.3

Bunkasar kasuwanci tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen nahiyar Afirka ya kai na kudi dalar Amurka biliyan 1.3 Shugaban cibiyar hada-hadar kasuwanci tsakanin Iran

Bunkasar kasuwanci tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen nahiyar Afirka ya kai na kudi dalar Amurka biliyan 1.3

Shugaban cibiyar hada-hadar kasuwanci tsakanin Iran da Afirka, Masoud Barhaman ya bayyana cewa: Adadin hada-hadar kasuwanci tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen nahiyar Afirka a halin yanzu ya kai na kudi dalar Amurka biliyan daya da miliyan 300. kuma ya jaddada bukatar yin kokarin samar da tsare-tsare wadanda suka dace don daukaka wannan mataki tare da bunkasa shi.

A cikin bayaninsa yayin taron “Damar Kasuwanci a Nahiyar Afirka”, wanda kungiyar ‘yan kasuwa ta Zanjan ta shirya (a lardin Zanjan – da ke shiyar arewa maso yammacin kasar Iran), Barhaman ya bayyana cewa: Nahiyar Afirka na cike da ma’adinai da yalwar yanayi na dabi’a, kyakkyawan muhalli da albarkatun noma masu yawa. Don haka ya bayyana takaicinsa kan yadda yawan huldar kasuwanci tsakanin Iran da kasashen nahiyar ta Afirka ba ta wuce dala biliyan daya da miliyan 300 ba.

Jami’in na Iran ya yi nuni da cewa: Dala biliyan 1 na wannan kudade yana zuwa ne sakamakon fitar da kayayyaki zuwa kasashen Afirka da sauran kasashen ketare a jimillar kayayyakin da Iran ke shigowa da su daga wannan nahiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments