Kashim Shettima: Muna Fatan Za A Yafe Wa Nijeriya Basussuka

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta mayar da hankali wurin ganin an yafe wa Nijeriya da sauran ƙasashe masu tasowa

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta mayar da hankali wurin ganin an yafe wa Nijeriya da sauran ƙasashe masu tasowa basussukan da ake binsu.

Sanata Kashim Shettima wanda ke wakiltar Shugaba Bola Tinubu, ya faɗi hakan cikin jawabinsa a gaban Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya a taronta da ke gudana a birnin New York na Amurka.

Ya bayyana cewa “Dole ne mu tabbatar da cewa duk wani sauyi da za a kawo ga tsarin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa ya haɗa da tsarin sauƙaƙa bashi, domin bayar da damar samun ci gaba mai ɗorewa ta ɓangaren kuɗi.

“Ƙasashen da ke kudancin duniya ba za su samu wani ci gaban tattalin arziki ba, ba tare da rangwame na musamman ba da kuma nazarin nauyin bashin da suke ciki a halin yanzu,” in ji Shettima.

Sauran batutuwan da mataimakin shugaban ya taɓo a jawabin nasa sun haɗa da neman haɗin kan Majalisar Ɗinkin Duniya wajen ganin an mayar da kuɗaɗen sata da waɗanda aka fitar da su zuwa manyan ƙasashe ba bisa ƙa’ida ga ƙasashen da aka sato su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments