Manyan kasashe 3 da suka hada da Spain da Ireland da Norway sun sanar da cewa sun amince da kasar Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya habarta cewa, manyan jami’an kasashen Spain, Ireland da Norway sun sanar da amincewa da Palastinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
Duk da matsin lambar da Isra’ila ke yi da kuma kin amincewar Amurka, kasashen Turai uku sun amince da Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
Majalisar ministocin Spain karkashin jagorancin Firayi Minista Pedro Sanchez ta sanar da amincewa da Falasdinu a matsayin kasa a hukumance.
Sanchez ya sanar a gaban majalisar zartaswar cewa, wannan mataki shi ne kadai hanyar samun zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Firaministan Spain ya sanar da cewa amincewa da ‘yantacciyar kasar Falasdinu mataki ne na tabbatar da adalci a tarihi.
A yau ne ita ma gwamnatin Ireland ta amince da shirin amincewa da Falasdinu a matsayin kasa. Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta amince da kulla cikakkiyar huldar diplomasiyya tsakanin Dublin da Ramallah.
Bayan Spain da Ireland, gwamnatin Norway ta sanar da cewa ta amince da Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta a hukumance.