Kasashen Turai 4 Sun Fitar Da Bayanin Hadin Gwiwa  Na Yin Tir Da HKI Dangane Da “UNRWA”

Kasashen Ireland, Norway, Slovania da Sapain sun fitar da bayanin hadin gwiwa akan matakin da  majalisar HKI ta  “Knesset” ta dauka na haramta ayyukan hukumar

Kasashen Ireland, Norway, Slovania da Sapain sun fitar da bayanin hadin gwiwa akan matakin da  majalisar HKI ta  “Knesset” ta dauka na haramta ayyukan hukumar agajin Falasdinawa ta ( UNRWA ).

Ma’aikatar harkokin wajen Ireland ta wallafa bayanin hadin gwaiwar  a shafinta na Internet da a ciki ya kunshi cewa; hukumar ta “UNRWA” ta Majalisar Dinkin Duniya ce da take aiki a Falasdinu domin taimaka wa miliyoyin Falasdinawa ‘yan gudun hijira.

Bayanin ya cigaba da cewa, an kafa wannan hukumar ne domin ta rika tafiyar da rayuwar Falasdinawa ‘yan gudun hijira, da a wannan yanayin da ake ciki su ka fi bukatuwa da ita.

Kasashen 4 sun sha alwashin cigaba da bai wa Falasdinawa taimakon da suke bukatuwa da shi ta hanyar wannan hukumar,kuma sauran kasashen da wannan hukumar take da rassa a cikinsu, za su cigaba da bayar da taimakonsu.

A jiya Litinin ne dai majalisar HKI ta yi dokar hana duk wasu ayyuka da su ka shafi wannan hukumar ta ( UNRWA) a fadin Falasdinu dake karkashin mamaya.

Shekara daya bayan kirkirar HKI ne wato a 1949 MDD ta samar da “UNRWA” domin taimakawa Falasdinawan da aka kora daga garuruwansu da gidajensu. Ayyukanta kuma sun shafi koyarwa,kiwon lafiya a Gaza da kuwa yammacin kogin Jordan, haka nan a kasashen da ‘yan  gudun hijirar Falasdinawa suke.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments