Kasashen Musulmi Sun Yi Tir Da Harin Isra’ila A Asibitin Gaza

Harin da Isra'ila ta kai a Asbitin Nasser ya kashe akalla Falasdinawa 6.

Ministocin harkokin waje daga kasashen Musulmi da Larabawa 18, ciki har da Saudiyya, Turkiyya, Masar da Pakistan, sun yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai wa asibitin Nasser da ke kudancin Gaza, suna masu cewa ya karya dokar jin kai ta duniya kuma ya jefa lafiyar marasa lafiya da ma’aikatan lafiya cikin hadari.

A cikin wata sanarwa ta bai daya a ranar Asabar, ministocin sun ce harin ya keta kariyar musamman da aka ware wa cibiyoyin lafiya da ma’aikata a karkashin dokar jin kai ta duniya.

Harin sama da Isra’ila ta kai a Asbitin Nasser da ke kudancin Gaza ya kashe akalla Falasdinawa shida, ciki har da likitan tiyata, a safiyar ranar 12 ga Nuwamba.

Harin ya kuma yi sanadiyyar jikkata akalla mutane 20, a cewar Ma’aikatar Lafiya da Tsaron Farar Hula ta Gaza.

Kasashen Aljeriya, Djibouti, Turkiyya, Masar, Indonesia, Jordan, Kuwait, Lebanon, Libya, Mauritania, Oman, Pakistan, Palestine, Qatar, Saudiyya, Somaliya, Sudan, da Hadaddiyar Daular Larabawa suna daga cikin kasashen da sukayi Allah wadai da harin.

Ministocin sun kuma yi tir da hare-haren da Isra’ila ke kai wa fararen hula Falasdinawa, ciki har da hare-haren sama da jiragen sama da ke kai hari kan matsugunan wucin gadi ga mutanen da suka rasa matsuguni.

Sun amince cewa irin wadannan ayyuka suna kawo cikas ga tsagaita wuta da kuma kokarin kasashen duniya da nufin maido da tsaro da kwanciyar hankali a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted