Ministan ilimi da kere-kere na Iran Husain Simayi, wanda ya gana da jakadan kasar Turkiya anan Iran Hijabi Kalanjik ya bayyana azamar kasashen biyu domin yin aiki a wadannan fagagen.
Ministan ilimin da kuma fasahar kere-kere na Iran ya kuma ya kuma ce; Iran tana bayar da muhimmanci ga jami’o’in Turkiya wadanda a bisa ma’aunin duniya suke da matsayi na koli, suna kuma gabatar da su ga daliban kasar da suke son yin karatu a waje.
A nashi gefen, jakadan kasar Turkiya a Iran ya bayyana cewa; Kasashen biyu sun yi tarayya akan abubuwan da dama, tare da cewa Ankara tana bayar da muhimmanci ga alakar ilimi da al’adu da Iran.
A yayin wannan ganawar, bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayi akan kafa tsangayoyin ilimi na hadin gwiwa domin yin nazari da bincike da kuma warware matsalolin daliban da suke karatu a kasashen biyu.
Daga cikin abubuwan da bangarorin biyu su ka tattauna da akwai yadda za a kara saukakewa daliban kasashen biyu kai da komowa.