Kasashen Iran Da Masar Sun Jaddada Aniyarsu Ta Ganin Sun Kyautata Alakar A Tsakaninsu

Kasashen Iran da Masar sun tabbatar da ci gaba da tuntubar juna da nufin dawo da harkokin siyasa da alakar da ke tsakaninsu A wata

Kasashen Iran da Masar sun tabbatar da ci gaba da tuntubar juna da nufin dawo da harkokin siyasa da alakar da ke tsakaninsu

A wata tattanawa tsakanin ministan harkokin wajen kasar Masar Badr Abdel Ati da takwaransa na Iran Abbas Araqchi ta hanyar wayar tarho, Badr Abdel Ati ya taya Abbas Araqchi murnar nadin da aka yi masa a matsayin sabon ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, tare da yi masa fatan samun nasara.

Ministan harkokin wajen Masar ya gabatar da rahoto kan kokarin diflomasiyya da kasarsa ta yi a ‘yan kwanakin nan na dakatar da yakin da ake yi da zirin Gaza tare da aikewa da kayan agajin jin kai na kasa da kasa, ya kuma jaddada bukatar dukkanin bangarorin da su yi kokarin hana yaduwar yakin a yankin.

A nashi bangaren, Araqchi ya yi godiya ga takwaransa na Masar don kiran da ya yi masa na taya shi murna, ya kuma nuna jin dadinsa ga kokarin Masar a shawarwarin neman tsagaita wuta a zirin Gaza. Har ila yau ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada hakkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na mayar da martani kan ta’addancin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata a birnin Tehran na janyo shahadar shahidi Isma’il Haniyah.

Bangarorin biyu sun amince da ci gaba da tuntubar juna da fahimtar harkokin siyasa dangane da alakar da ke tsakanin kasashen biyu da ci gaba a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments