Ministan sufuri na kasar iran Mehrdad bazarpash da takwaransa na kasar Cuba Edwardo Dovila sun tattauna a nan birnin Tehran game da hanyoyin da za’a bi wajen kara fadada dagantakar dake tsakaninsu musamman a bangaren sufurin jiragen sama na ruwa da na kasa, ganin cewa da dama daga cikin yarjeniyoyin da aka sanyawa hannu a kai a baya ba’a yi aiki da su ba.
Ana sa bangaren ministan sufuri na kasar iran ya bayyana cewa iran a shirye take tayi aiki tare da kasar Cuba a bangaren gyaren jiragen sama. a bagaren sufurin jiragen ruwa ma tana da damarmaki da yawa da kasashen biyu za su ci gajiyar juna.
Daga karshe dukkan bangarorin biyu sun bayyana cewa babban hadafin ganawar shi ne bibiyar yarjeniyoyin da aka kulla a baya tsakanin kasashen biyu da kuma mataken da za’a bi wajen ganin an yi aiki da su