Kasashen Afrika Dake Fama Da Malaria, Sun Sha Alwashin Murkushe Mace-macen Cutar

Kasashen Afrika dake fama da cutar zazzabin malaria sun sha alwashin murkushe mace-macen da cutar ke yanjowa. Wannan bayyanin ya fito ne a jawabin bayan

Kasashen Afrika dake fama da cutar zazzabin malaria sun sha alwashin murkushe mace-macen da cutar ke yanjowa.

Wannan bayyanin ya fito ne a jawabin bayan taron da ministocin lafiya na kasahsen, suka gudanar a Jamhuriyar Kamaru.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar cewa yankin Afrika ne ke samar da kashi 95 na mace-macen da ake yi sakamakon malaria.

Kasashen da suka fi fama da cutar sun hada da Burkina Faso da Kamaru da DR Congo da Ghana da Mali da Mozambique da Nijar da Nijeriya.

Sai kuma Sudan da Uganda da kuma Tanzania.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments