Kasashe Na Tir Da Hare-haren Isra’ila Kan Iran

Kasashen duniya sun fara mayar da martini game da jarein hare-haren da Isra’ila ta kai wa Iran a cikin daren jiya wayewar safioyar Asabar din

Kasashen duniya sun fara mayar da martini game da jarein hare-haren da Isra’ila ta kai wa Iran a cikin daren jiya wayewar safioyar Asabar din nan.

A cikin wata sanarwa data fitar ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya ta yi kakkausar suka, inda ta yi tir da harin da Isra’ila ta kai kan Iran.

Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta kuma yi kira da a kwantar da hankali game da al’amarin.

Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta jaddada cewa harin da aka kai wa Iran ya zama cin zarafi ne da keta hurumin kasar da kuma keta dokokin kasa da kasa.

Saudiyya ta kuma yi gargadi game da ci gaba da karuwae tashe tashen hankula a yankin.  

Ita ma “Malaysia ta yi tir da harin inda ta bukaci a kai zuciya nesa.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce ayyukan da Isra’ila ke ci gaba da yi za su ci gaba da yin tasiri, a fannin tsaro da zaman lafiyar yammacin Asiya a nan gaba, lamarin da zai kara kusantar da yankin a cikin wani rikici.

Pakistan ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya, ta kira hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Iran a matsayin “tada rikici”

Ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta yi Allah-wadai da harin da Isra’ila ta kai wa Iran cikin dare, tare da bayyana hakan a matsayin “hatsarin ga  yankin.

Ta yi kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki matakin gaggawa don dakatar da abin, tare da yin kira ga kasashen duniya da su shiga tsakani don hana ci gaba da tada zaune tsaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments