Gwamnatin kasar masar ta tabbatarwa gwamnatin Falasdinawa kan cewa tana goyon bayan falasdinawa a cikin dawo da hakkinsu, na kafa kasarsu mai cikekken yanci wacce take da gabacin birnin Qudus a matsayin babban birnin Kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mostafa Madbouly ministan harkokin wajen kasar Masar yana fadar haka a lokacin ganawarsa da tokwaransa na gwamnatin Falasdinawa a Ramallah Mohammada Mustafa a birnin Alkahira.
Madbouly ya kara da cewa gwamnatin kasar Masar tana son ganin an gaggauta sake ginza Gaza da kuma maida rayuwa kamar yadda take a gaza da gaggawa.
Ya ce kasashen larabawa ba zasu taba yarda da kasar Falasdina kasa da yarjeniyar 4 ga watan Yunin shekara ta 1967.
A ranar Talata 4 ga watan Maris da muke ciki ne za’a gudanar da taron gaggawa na kungiyar kasashen larabawa a birnin Alkahira na kasar Masar don tattauna halin da Falasdinawa suke ciki musamman a Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan.