Kasar Iran Ta Yi Watsi Da Zarge-Zargen Da Kwamitin Alkalan Hukumar AIEA Ta Yi Kanta

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da zarge-zargen da kwamitin alkalan Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ya yi kanta Jakadan kasar Iran

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da zarge-zargen da kwamitin alkalan Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ya yi kanta

Jakadan kasar Iran na din din din a Majalisar Dinkin Duniya, Amir sa’id Irawani, ya aike da sakon wasika ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya inda a ciki ya yi watsi da zarge-zargen da kwamitin alkalan hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa ya fitar kan kasar Iran.

Jakadan kasar ta Iran ya aike da sakon ne ga shugaban kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da kuma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, yana mai bayyana cewa, har yanzu kungiyar Tarayyar Turai tana zargin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da rashin kiyaye yarjejeniyar da take wajibi a kanta, wadda aka gindaya kanta a karkashin yarjejeniyar nukiliya, tana zargin Iran da yin watsi da yarjejeniyar da gangan.

Irawani ya jaddada cewa: Matsayin Iran shi ne gudanar da matakan da suke ingantattu da suka yi daidai da hakkokinta kamar yadda doka ta 26 da 27 ta yarjejeniyar nukiliyar ta tanada a matsayin martani ga ficewar Amurka daga yarjejeniyar.

Jakadan na Iran kuma wakilinta na din-din-din a Majalisar ta Dinkin Duniya ya kara da cewa a cikin sakonsa: Manufar wannan mataki na Iran da aka dauka tsawon shekara guda bayan ficewar Amurka ba bisa ka’ida ba da kuma gazawar kasashen Turai uku wajen aiwatar da alkawurran da suka dauka na dage takunkumai kan Iran a fili yake, wanda hakan yana bayyana maido da daidaito a cikin wajibai da suka doru a kan kowane bangare da kare muradun juna da ke kunshe cikin yarjejeniyar ta nukiliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments