Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan yankunan birnin Damascus fadar mulkin kasar Siriya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i, ya yi kakkausar suka kan hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan wasu yankunan birnin Damascus fadar mulkin kasar Siriya, wanda ya yi sanadin shahada da jikkatar mazauna yankunan da suka hada da ‘yan Siriya da Falasdinawa da dama, tare da lalata ababen more rayuwa da suka hada da hanyoyi da gadoji da suka hada Siriya da Lebanon.
Baqa’i ya yi ta’aziyyar ga gwamnati da al’ummar Siriya da kungiyar Jihadul Islami ta Falastinu da kuma iyalan shahidan, yana mai fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya kuma jaddada cewa: Fadada hare-haren wuce gona da iri da laifuffukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa kan kasashen da suke makwabtaka da su, da kuma cin zarafi da musguna hakkokin kasa da kasa ta hanyar keta hurumin kasashe misalin Jamhuriyar Larabawa ta Siriya, al’amura ne da ake daukarsu a matsayin cin zarafi a fili, kamar yadda yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya ya tanada, don haka kasar Iran tana bukatar daukar matakin gaggawa daga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya don dakatar da wadannan ayyukan ta’addanci tare da dorawa kungiyar ‘yan ta’addan sahayoniyya alhakin cin zarafin da kumahukunta ta.