Ministan Harkokin Wajen Iran ya shawarci shugaban Amurka da ya mayar da yahudawan sahayoniyya zuwa Greenland
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya yi kan ba da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, maimakon haka Araqchi ya ba da shawarar kwashe ‘yan sahayoniyya Greenland.
Ministan harkokin wajen Iran ya yi ishara da haka ne a wata hira da kafar yada labarai ta Sky News, yana mai bayyana cewa: A mahangar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a bayan da Trump ya shiga fadar White House a farkon wa’adinsa ya gabatar da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, amma kokarinsa ba ta yi nasara ba. hakan yana nufin rashin yiwuwar korar Falasdinawa daga tushensu.
Arqchi ya kuma mayar da martani ga tashar ta Sky News kan tambayar ‘yancin da ‘yan sahayoniyya suke da shi na rayuwa, inda ya ce: “Kowane dan Adam na da ‘yancin rayuwa, amma babu wanda ke da hakkin ya mamaye kasar wani, wannan kasa ta Falasdinawa ce, dole ne Falasdinawa su yanke shawara da kansu game da makomar kasarsu”.