Kasar Iran Ta Jaddada Karfafa Kyakkyawar Alakarta Da Rasha Domin Bunkasa Ci Gabansu

Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Kyakkyawar alakar da ke tsakanin Iran da Rasha ya ginu ne a kan kare maslahar juna a

Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Kyakkyawar alakar da ke tsakanin Iran da Rasha ya ginu ne a kan kare maslahar juna a tsakaninsu kuma za ta ci gaba

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Baqiri ya bayyana alakar da ke tsakanin Iran da Rasha da cewa ta ginu ne a kan tsari da maslaha da zasu kare muradun kasashen biyu, yana mai jaddada cewa; Wannan kyakkyawar alaka zata ci gaba da wanzuwa kan tubalin kare maslahar junansu a nan gaba.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da Ali Baqiri yake gudanar da ziyara a birnin Nizhny Novgorod na kasar Rasha domin halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar BRICS, inda ya yi wata ganawa ta musamman da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov a jiya litinin.

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya yaba da sakon ta’aziyya da jaje da jami’an kasar Rasha suka aike da kuma halartar taron bankwana da gawar shugaban kasar Iran da ministan harkokin wajen kasar da mukarrabansu da suka yi shahada. Yana mai jaddada alakar Iran da Rasha da cewa: Ta ginu ce a kan kyawawan manufofi da ingantattun muradun kasashen biyu kuma za ta ci gaba a nan gaba.

Baqiri ya yi ishara da fahimtar juna da matsaya daya da suke dauka gami da taimakekkeniya a tsakanin kasashen biyu a tarukan yanki da na kasa da kasa, kuma ya jaddada wajabcin kara yin kokarin dakile laifukan da yahudawan sahayoniyya suke yi a Gaza da Rafah na Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments