Shugaban kasar Iran sayyid Ibrahim Ra’aisi ya aike da sakon taya murna ga gwamnati da alummar kasar Zimbabwe na zagayowar ranar samun yancin kasar daga hannun yan mulkin mallakar birtaniya a shekara ta 1980.
Har ila yau shugaban kasar ta Iran ya fadi cewa dangantakar dake tsakanin iran da Zimbabwe a shekarun baya bayan nan sun kara kyautata , manyan jami’an gwamnatin kasashen biyu sun tattauna game da hanyoyin da za’a bi wajen ganin an kara fadada dangantaka tsakanin kasashen biyu,
Bisa Tsarin mau’amalar Iran da sauran kasashen duniya ba ta da ra’ayin kulla dangantaka ta bangare daya,musamman kan kasashen turai, don haka kulla hulda da kasahen Afrika da Asiya suna daga cikin bangaren da ta fi ba fifiko, domin nahiyar Afrika kasuwace da ta dace wajen sayar da kayayyakin da aka kera a kasar iran, wannan yasa alaka da kasashen afrika take da matsayin na musamman a siyasar harkokin wajen Iran.