Karfin Diblomasiyyar Kasar Iran Ce Ya Sa Ta Bayyana Karfin Kayakin Yakinta Wa kasashen Yankin

Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka

Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na kasar yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, iya diblomasiyyar kasar Iran a tsakanin  kasashen yankin, ya tabbatar da karfin da kasar take da shi a fagen karfin soje.

Kuma ta tabbatar da cewa zata iya kula da al-amuran tsarom da kuma tabbata shi a yankin. Sayyari yace an gudanar da atisayen na sojoji kimani rundunonin fiya da 100 inda suka yi musayar tunani da dabar barun yaki a tsakaninsu, inda da dama daga cikinsu sojojin kasashen waje ne.

Yace a cikin wadannan atisai daban-daban sun yi amfani da sabbin makamai da kasar ta kera da kuma sabbin dabarbarun yaki. Daga karshe Sayyari ya bayyana cewa mai suna ‘Zulfikar’ sojojin kasar Iran zasu nuna karfinsu a fagen kayakin aikin zamani da kuma sabbin dabarbarun yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments