Manyan kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa da dama sun tsawaita dakatar da zirga-zirgar jiragensu zuwa yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta mamaye, a daidai lokacin da kasar Yemen ta sha alwashin daukar mataki kan kasar.
Kamfanin jirgin sama na Air France ya sanar cewa, bayan dakatarwar da aka yi na tsawon watanni, zai ci gaba da dage zirga-zirgar jiragensa zuwa yankunan Falasdinu da aka mamaye har zuwa ranar 24 ga watan Mayu.
Da farko Air France ya yi niyyar dawo da zirga-zirgar jirage a wannan makon, amma ya zabi karin jinkirta hakan.
Kamfanin Lufthansa da SWISS, Austrian Airlines, Brussels Airlines da Eurowings, su ma sun tsawaita dakatar da zirga-zirgar jiragensu zuwa yankunan da aka mamaye.
“Saboda halin da ake ciki yanzu, kamfanin Lufthansa zai dakatar da zirga-zirgar jiragensa zuwa Tel Aviv har zuwa ranar Lahadi 8 ga watan Yuni,” maimakon ranar 25 ga Mayu.
Kamfanin jiragen sama na Burtaniya EasyJet, wanda ya hada da EasyJet UK, EasyJet Switzerland da EasyJet Turai, shi ma ya dage ci gaba da zirga-zirgar jiragensa har zuwa akalla 30 ga watan Yuni.
Sauran kamfanonin jiragen sama na Turai su ma sun bi sawu, suna tsawaita dakatarwa ko soke tashin jirage.
Yeman dai ta sha kai hare-hare a filin jirgin saman Ben Gurion, mafi muhimmanci ga Isra’ila, da makamai masu linzami domin nuna goyan baya ga al’ummar Gaza da shan ukuba daga Isra’ila.