Kamfanin  Mai Na Gwamnatin Najeriya Ya Kara Farashin Litar Mai Zuwa Naira 897

A wata sanarwa da kamfanin mai na Najeriya, NNPCL yabayar, ya sanar da sabon farashin litar man fetir. A wata sanarwa da kamfanin ya aike

A wata sanarwa da kamfanin mai na Najeriya, NNPCL yabayar, ya sanar da sabon farashin litar man fetir. A wata sanarwa da kamfanin ya aike wa manema labarai, kamfanin ya ce daga yau ranar 3 ga watan Satumban 2024, kamfanin ya ƙara kuɗin litar man fetir daga naira 617 zuwa 897.

Jim kadan bayan sanarwar ne  wasu gidajen maI a Najeriya suka sauya farashin litar zuwa sabon da kamfanin ya sanar a wannan  Talata 3 ga watan Satumba.

Hakan  dai na zuwa ne kwana guda bayan da kamfanin man na kasa ya bayyana cewa yana fuskantar matsalar karancin kudi, wani abu da ya sa ‘yan Najeriya hasashen kamfanin na kokarin sanar da sabon farashi ne.

Tun kafin sanar da sabon farashin dogayen layukan ababan hawa sun mamaye gidajen mai a biranen Abuja da Legas da sauran manyan birane na kasar.

Bayan da gwamnatin shugaba Tinubu ta sanar da janye tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023, mutanen  Najeriya ke fuskantar sauye-sauye a farashin man wanda kuma ke yin tasiri kai tsaye a cikin sauran bangarori na rayuwa, da kuma farashin kayan masarufi.

Duk da cewa dai Nijeriya na cikin kasashen da suke samar da danyen man fetur a duniya, sai dai ba ta iya tace shi sakamakon yadda akasarin mataun main a kasar suka tsaya cak, duk kuwa da makuden kudaden da ake warewa a cikin kowane kasafin shekara domin gyaran su, yayin da wasu masanan ke cewa, kudin gyaran matatun maid a aka ware a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, sun isa a gina wasu sabbin matatun mai da su a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments