Shugaban kasar Kamaru, Paul Biya, ya ayyana ranar 7 ga watan Fabarairu na 2027 a matsayin ranar da za’a gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi.
Matakin na zuwa ne bayan fiye da shekaru biyu na tsawaita wa’adin shugaban kasa.
An tsawaita wa’adin ‘yan majalisar dokoki har zuwa 20 ga Disamba, 2026, da kuma na kansilolin kananan hukumomi har zuwa 28 ga Fabrairu, 2027.
Za a gudanar da zaben 7 ga Fabrairu, 2027, sama da shekara guda bayan zaben shugaban kasa na karshe, inda aka ayyana Paul Biya a matsayin wanda ya yi nasara da kashi 53% na kuri’un.
‘Yan adawa sun sami fiye da kashi 45% na kuri’un, ciki har da fiye da kashi 35% ga Issa Tchiroma.
An dakatar da jam’iyyar Tchiroma, ta (FSNC), na tsawon watanni uku a karshen watan Oktoba 2026 saboda zargin tayar da zaune tsaye.”
A zaben ‘yan majalisa na karshe, a shekarar 2020, jam’iyyar CPDM mai mulki ta lashe kujeru 152 daga cikin kujeru 180 a Majalisar Dokokin kasar, A yayin da kuma Jam’iyyar ke da iko da manyan biranen kasar.