Majalisar tsarin mulkin kasar Kamaru ta amince da matakin haramta wa babban abokin hamayyar shugaba Paul Biya Maurice Kamto tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 12 ga watan Oktoba.
A watan Yulin da ya gabata ne dai hukumar zabe ta fitar da Kamto daga jerin sunayen ‘yan takarar da aka amince da su. Hukumar ta bayyana cewa an hana Kamto tsayawa takara ne saboda ya tsaya takara a karkashin tutar jam’iyyar Manyedem, wadda ita ma ta goyi bayan dan takara na biyu.
Kamto ya daukaka kara a cikin kwanaki biyu. Sai dai shugaban majalisar tsarin mulkin kasar, Clement Atangana, ya amince da hukuncin haramta masa tsayawa takarar. Ba a iya samun damar jin ta bakin Kamto ba don yin tsokaci, a cewar Reuters.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce matakin da hukumar zaben kasar Kamaru ta dauka na haramta wa Kamto tsayawa takara ya haifar da damuwa game da sahihancin tsarin zaben kasar.
Dubban masu zanga-zanga ne suka taru a kofar Majalisar Tsarin Mulki a ranar Litinin domin nuna goyon bayansu ga Kamto, amma ‘yan sanda sun tarwatsa su da hayaki mai sa hawaye.
Kwamishinan ‘yan sandan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa “an kama mutane da dama kuma suna ci gaba da tsare su domin gudanar da bincike.
A zaben da ya gabata a shekarar 2018, Kamto ya zo na biyu da kashi 14% na kuri’un da aka kada, yayin da Biya ya samu gagarumin rinjaye, wanda ‘yan hamayya da ma wasu bangarori na kasa da kasa ke ganin cewa an tabka magudia zaben.