Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Allah Wadai Da Harin Isra’ila A Lebanon

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi kakkausar suka tare da yin Allah wadai kan hare-haren da ‘yan sahayoniyya suka kai a kudancin kasar Lebanon Kakakin

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi kakkausar suka tare da yin Allah wadai kan hare-haren da ‘yan sahayoniyya suka kai a kudancin kasar Lebanon

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya yi kakkausar suka tare da yin tofin Allah tsine da kakkausar murya kan hare-haren wuce gona da iri da ‘yan ta’addan yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan wasu yankuna da dama a kudancin kasar Lebanon da suka janyo shahadar daruruwan mutanen kasar da ba su ji ba su gani ba.

Kan’ani ya kuma yi kakkausar suka kan shirun da Amurka ke yi da ma hadin kan da suke yi da kuma wasu kasashen yammacin turai masu goyon bayan ‘yan sahayoniyya, yana mai gargadin ci gaba da aikata laifukan yaki da wannan lalatacciyar gwamnati take yi a kan al’ummar Falastinu da kuma yunkurin fadada yakin da ake yi a yankin baki daya, yana mai jaddada gargadin mummunan sakamakon da wannan kasada na ‘yan sahayoniyya zata janyo.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ya kuma bayyana wadannan hare-haren a matsayin hauka, yana mai nuni da cewa gano laifukan da yahudawan sahayoniyya suka aikata a cikin shekarar da ta gabata ya sanya wannan lalatacciyar gwamnati tana ci gaba da tafka kura-kurenta ci gaba da aikata laifuka da munanan manufofinta na kisan kare dangi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments