Kan’ani: Isra’ila Ba Za Ta Taba Murmurewa Daga Harin Guguwar Al-Aqsa Ba  

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar  kasar Isra’ila ba za ta koma kafin harin Ambaliyar Al-Aqsa ba Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar  kasar Isra’ila ba za ta koma kafin harin Ambaliyar Al-Aqsa ba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa: Daidaiton dabarun da aka samu a yankin Gabas ta Tsakiya ya canza zuwa ga masalahar Falasdinu, al’ummarta da kuma kungiyoyin gwagwarmayarta bayan harin ambaliyar Al-Aqsa, kuma haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta taba komawa kamar yadda take kafin harin Ambaliyar ta Al-Aqsa ba.

A wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, Kan’ani ya bayyana cewa: Babban muhimmin sauyin da harin Ambaliyar Al-Aqsa ya haifar a cikin batun Falasdinu, shi ne mayar da harin a matsayin muhimmin batu na yankin da na kasa da kasa. Har ila yauharin na Ambaliyar Al-Aqsa ya dawo da batun Palastinu a fagen kasa da            kasa, wanda yahudawan sahayoniyya da abokan su tsawon shekarun baya-bayan nan suka yi kokarin juya akalansa zuwa ga wani batu maras muhimmanci da aka manta da shi a cikin tsare-tsaren yankin da na duniya.

A halin yanzu babu wanda ya dauki batun Falastinu a matsayin rufaffen al’amari ko kuma aka manta da shi a cikin tsare-tsaren sasantawa kuma sharadin kyautata alaka da ‘yan sahayoniyya. Har ila yau, ba zai yiwu a yi imani da cewa za a iya warware matsalar Falasdinu ta hanyar yin shawarwarin sasantawa tsakanin yahudawan sahayoniyya da wasu kasashen yankin ba, tare da mayar da matsayin Falasdinu tamkar ba shi da wani tasiri.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments