Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatima Mohajerani ta yi Allah wadai da harin da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan yankin kasar Iran, tare da kara wa da cewa: Wadannan ayyukan wuce gona da iri na ‘yan sahayoniyya zai kara hadin al’ummar kasar Iran.
A taron manema labarai da ta gudanar a yau Talata, Fatima Mohajerani ta yi ishara da yadda yahudawan sahayoniyya suka kai hari kan yankunan kasar Iran, ta kuma kara da cewa: Wadannan ayyukan wuce gona da ‘yan sahayoniyya suka aikata lamari ne da zai kara karfafa hadin kan al’ummar kasar Iran. Mohajerani ta kuma jaddada cewa: Babban kuskure ne yahudawan sahayoniyya su yi tunanin cewa, Za su iya yin tasiri wajen janyo gibi a hadin kan al’ummar da irin wadannan ayyuka, tana mai jaddada cewa: Jajirtattun dakarun kasar Iran sun yi yaki sosai, kuma a kodayaushe a fadake suke don kare manufofi da al’ummar kasarsu.