Kakakin Bangaren Sojin Kungiyar Hamas Ya Jinjina Harin Iran Kan Isra’ila

Kakakin bangaren sojin Izzuddeen Al-Qassam ya bayyana cewa: Harin daukan fansa na “Alkawarin Gaskiya” ya firgita makiya ‘yan sahayoniyya Kakakin rundunar Izzuddeen Al-Qassam bangaren soji

Kakakin bangaren sojin Izzuddeen Al-Qassam ya bayyana cewa: Harin daukan fansa na “Alkawarin Gaskiya” ya firgita makiya ‘yan sahayoniyya

Kakakin rundunar Izzuddeen Al-Qassam bangaren soji na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, Abu Ubaida a cikin jawabinsa a bikin cika shekara guda da fara yakin “Guguwar Al-Aqsa” ya tabo batutuwa da dama musamman gwagwarmayar Falasdinawa da yakin goyon bayan gwagwarmaya, da hare-haren Iran, da hare-haren kisan gilla kan jagororin gwagwarmaya, da kuma mai da hankali kan ci gaba da yakar ‘yan mamaya.

Abu Ubaida ya ce a cikin jawabinsa na faifan bidiyo na tunawa da ranar da aka fara yakin “Guguwar Al-Aqsa” a ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, ya bayyana cewa: Suna jawabi ne ga al’umma daga Gaza tushen gwagwarmaya da turjiya, da suka gagari makiya ‘yan sahayoniyya, yana mai jaddada cewa: Shekarar da ta gabata tun lokacin da ƙwararrun mayaka suka samu nasarar kan na’urorin zamani mafi girman fasaha.

Abu Ubaida ya yaba da matakan gwagwarmaya da tsayin daka na al’ummar Falastinu, yana mai jaddada cewa tsayin daka ne na al’ada duk kuwa da halin ko-in kula da makwabtansu suke nuna wa, da tsoron da kungiyoyi suke yi na fuskantar makirce-makirce, duk kuwa da matsa kaimi kan ayyuykan zaluncin da makiya suke aiwatarwa kan al’ummar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments