Search
Close this search box.

Kafafen Yana Labarai Na HKI Suna Izgili Da Shuwagabannin Kasar Dangane Da Yaki A Gaza

Murabus wanda babban kwamandan sojojin HKI yake a kwanakin da suka gabata, saboda sabani da ta kunno kai a tsakaninsu, da kuma yadda suka kasa

Murabus wanda babban kwamandan sojojin HKI yake a kwanakin da suka gabata, saboda sabani da ta kunno kai a tsakaninsu, da kuma yadda suka kasa samun nasara a kan kungiyar Hamas bayan kwanaki 200 da fara yaki a gaza.

Labarin ya kara da cewa kafafen yada labarai a haramtacciyar kasar suna izgila da shuwagabannin  kasar bayan da suka kasa cika alkawulanda suka daukawa mutanen kasar na samun nasara a kan kungiyar Hamas da kuma dawo da yahudawan da suke tsare a hannun kungiyar ta Hamas.

Tasha ta 14 ta kasar ta na ci gaba da sukan shuwagabannin kasar taa kuma izgili da su. Banda haka tana ganin gazawar sojojin kasar wajen samun nasara a kan Jamas ya tabbatar da cewa ba zasu iya samun nasara a kan kungiyar Hizbullah daga areawacin kasar ba.

Har’ila yau tasha ta 13 ta kasar ta sake nanata alkawulan da Firai ministan kasar Benyamin Natanyahu yayi na samun nasara a kan Hamas watanni 6 da suka gabata. Ta kuma kara da cewa Natanyahu yana kara tsawaita yakin ne kawai don ya ci gaba da zama kan kujerar firaiministan kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments