Gwamnatin Kasar Iran ta bada sanarwan samun sabbin ci gaba a fagen fasaha da kuma kayakin da suka shafi makamashin Nukliya, wanda za’a baje kolinsa a ranar 9 ga watan Afrilu na wannan shekarar , wato ranar makamashin Nukliya ta kasa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto mataimakin shugaban kasa kuma shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Mohammad Eslami yana fadar haka a yau Lahadi. Ya kuma kara da cewa, masana fasahar nukliya ta kasar sun samar da sabbin ci gaba a fagen makamashin nukliya wadanda suka hada da magungun wadanda suka yi amfani da sinadarin Uranium don samar da su, da kuma ci gaba a fannonin ilmi da dama, duk tare da fasaha da kuma sinadarin nukliya.
Ranar makamashin Nukliya ta kasa a nan JMI dai, ita ce ranar da hukumar makamashin nukliya ta kasar take bayyana irin nasarori da kuma ci gaban da ta samu a fasahar nukliya da kuma kaddamar da abubuwan da ta samu tare da amfani da wannan fasahar a ko wace shekara.
Ya zuwa yanzu dai JMI ta samar da abubuwa da sama wadanda ta yi amfani da sinadarin Uranium ko makamashin nukliya kimani 100 a cikin kasar. Wanda ya hana da magunguna daban-daban fa ayyukan guda da tashe ruwa da wasu abubuwa da dama.