Jirgin Ruwa Dauke Da ‘Yan Maulidi 200 Ya Nutse A Neja

Jirgin ruwa dauke da mutane 200 da ya tashi a daren ranar Talata daga yankin Mundi zuwa Gbajebo don zuwa bikin Maulidi a karamar hukumar

Jirgin ruwa dauke da mutane 200 da ya tashi a daren ranar Talata daga yankin Mundi zuwa Gbajebo don zuwa bikin Maulidi a karamar hukumar Mokwa a Jihar Neja, ya nutse a ruwa.

https://hausa.leadership.ng/jirgin-ruwa-dauke-da-yan-maulidi-200-ya-nutse-a-neja/
Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne lokacin da jirgin ya doki wani itace da ke ƙarƙashin ruwan da ya taso a Kogin Neja.
Habibu Abubakar Wushishi, Daraktan Harkokin Yada Labarai da Tsare-tsare a Ma’aikatar Harkokin Jin-Kai, ya tabbatar da cewa lamarin.
Ya zuwa yanzu dai ba a san musababbin aukuwar hatsarin ba, amma ma’aikatar na aiki tare da Ma’aikatar Sufuri, Hukumar Kiyaye da Hadura ta Jihar Neja, da Hukumar Ruwa ta Kasa don gudanar da bincike.

Abdullahi Baba Arah, Babban Daraktan Hukumar Kula da Hadura ta Jihar Neja (NSEMA), ya bayyana cewa mazauna yankin sun ceto mutane 150 zuwa yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments