Jiragen Yakin HKI Sun Kashe mutane 3 da kuma jikada wasu 4 a kudancin kasar a jiya Asabar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kafafen yada labara na yankin kudancin kasar ta Lebanon suna fadar haka.
Labarin ya kara da cewa HKI ta yi amfani da makamai masu linzami wanda jirgin yaki na ” Drone” ya cilla kan wata mota a kan titi a garin Jarjoun da Iqlim Attuffah inda suka kashe mutane 3 sannan wasu kusa da motar guda 4 sun ji rauni.
Majiyar yahudawan ta bayyana cewa sun kashe wani kwamandan kungiyar Hizbullah ne, amma shaidu a yankin sun tabbatar da cewa duk wadanda HKI ta kashe ba mayakan kungiyar Hizbullah ne ba.
Wannan dai yana daga cikin ayyukan keta yarjeniyar tsagaita budewa juna wuta da aka kulla tsakanin HKI da kungiyar ta Hizbullah a cikin watan Jenerun da ya gabata.