Tarwatsewar Jiragen Ruwa 2 Ya Haddasa Gobara A Hormuz

wasu jiragen ruwa 2 sun fashe kuma ya haddasa tashin gobara a mashigar hormuz

Sojojin ruwa na dakarun kare juyin musulunci na iran sun bayyana cewa wasu tankokin mai guda biyu sun fashe bayan da suka ci karo da nakiyoyin ruwa, wannan yasa suka kama da wuta da hakan ya haddasa gobara a sanyi safiyar yau litinin a lokacin da suke kokarin satar hanyar wucewa a mashigar hurmzu duk da gargadin da jami’an tsaron iran suka yi

Yace jiragen mai din guda biyu sun yi kokarin bin hanyar da aka hana amfani da ita a kudancin horumuz ne da sojojin amurka ke jagoranta da kuma rakiyar jiragen saman amurka masu mamaya da babakere

Ya kara da cewa wasu tankokin mai guda 6 sun kama da wuta bayan sun ci karo da nakiyoyi kana kuma suka nutse a cikin teko a jiya lahadi a mashigar hormuz,

dakarun sojin na iran sun gargardi kamfanonin mai cewa hanyar kudanci da amurka ta kirkira a kusa da mashigar Hurmuz cike take da nakiyoyi kuma tana kewaye da katangar wuta, wanda ya amincewa jami’an sojin amurka da yin aiki tare da su a wajen  zai jefa tankokin mai cikin hadarin kamawa da wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted