Jihar Kogi da wasu 15 sun ƙalubalanci sahihancin hukumar EFCC a gaban kotun ƙoli

hausa.premiumtimesng.Kotun Ƙolin Najeriya ta sanya 22 ga watan Oktoba a matsayin ranar sauraren ƙarar da gwamnoni 16 na ƙasar suka shigar gabanta suna ƙalubalantar dokar

hausa.premiumtimesng.Kotun Ƙolin Najeriya ta sanya 22 ga watan Oktoba a matsayin ranar sauraren ƙarar da gwamnoni 16 na ƙasar suka shigar gabanta suna ƙalubalantar dokar da ta kafa hukumar Yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙi zagon ƙasa ta EFCC da wasu hukumomi biyu.

Alƙalai bakwai ne za su saurari shari’ar a ƙarƙashin jagorancin Uwani Abba-Aji, inda jihohin suka shiga sahun masu shigar da ƙara bayan jihar Kogi wacce ta fara shigar da ƙarar ta hannun alƙalin alƙalan jihar.

Jihohin da suka shiga sahun jihar Kogi sun haɗa da jihar Ondo, Edo.Oyo, Ogun, Nassarawa, Kebbi, Katsina, Sokoto, Jigawa, Enugu, Benue, Anambra, Fulato, Cross-River and Neja.

Jihohin sun yace sun dogara ne da kundin tsarin mulki kuma duk dokar da ta saɓa wa kudin tsarin mulki, to ba karɓaɓɓiya ba ce.

Masu shigar da ƙarar ta bakin lauyansu Joseph Nwobike wanda suke ƙarar gwamnatin tarayya kan rashin bin dokar da ta kafa EFCC ta shekarar 2024, inda suka ce ba a bin tanadin dokar sashe na 12 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da ka yi wa gyara.

A cewarsu Kundin Tsarin ya buƙaci cewa akwai buƙatar gabatar da buƙatar kafa hukumar ga majalisun dokokin jihohi kafin kafa EFCC wanda kuma suka ce sam ba a taɓa yin haka ba.

Sannan sun ce a bisa tanadin doka hukumar za ta yi aiki ne kaɗai kan jihohin da suka amince da ita kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin Najeriya. Don haka, duk hukuma makamanciyar EFCC da aka samar da ita ba tare da bin waccen doka ba, to haramtacciya ce.

A yayin da aka buɗe sauraron shari’ar a ranar Talata, lauyoyin da suke kare jihohin sun gabatar da muhawararsu, inda mafi yawa suka buƙaci a haɗe jawabisu ƙararsu cikin ta sauran da suka gabatar.

Alƙalin alƙalai na jihar Kogi, Abdulwahab Mohammed, ya ce akwai jihohin da ke so a haɗe ƙarar tasu wuri ɗaya da waɗanda ke son cin gashin kasu a shari’ar.

Don haka, ya nemi shawarar kotun kan sanar da su abin da ya dace su.

Jihohi 13 cikin 15 sun buƙaci a haɗe shari’ar waje ɗaya, sai dai johohi biyu rak ne suka nuna shawa’ar cin gashin kansu a shari’ar.

Daga nana ne mista Muhammed ya ce jihohin ke son cin gashin kansu suna da kwana bakwai domin shigar da ƙararsu daban kan wannan al’amari, inda kuma za a shigar da ƙara ta baiɗaya da sauran jihohin da su ma suka amince.

Daga nan ne mai shari’a Abba-Aji ta amince da roƙonsu tare da ɗage zaman shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Oktobar shekarar da muke ciki domin cigaba da suararon shari’ar.

Dambarwar da ake yi:

Gwamnonin sun bayyana cewa gwamnatin tarayya tare da Sashen Kula da Hada-hadar kuɗi (NFIU) ba su da hurumin ba da umarni ko ƙa’idoji kan tafi da kuɗaɗen gwamnatin jihar Kogi.

Sannan sun buƙaci EFCC da NFUI ko wata hukuma ta gwamnatin tarayya ba ta da ikon bincike ko neman wasu takardu ko gayyata ko kama wani bisa dalilin tasarrufin kuɗin jihar Kogi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments