Fiye da mashahuran mutane 160 ne da kuma ‘yan jarida suka shiga wani kamfen na neman gwamnatin Jamus da ta dakatar da fitar da makamai zuwa Isra’ila, inda ya zuwa wannan Laraba adadin wadanda suka sa hannu kan rakardar ya kai mutane 367.
Daga cikin wadanda suka rattaba hannu, wanda kungiyar fafutuka Avaaz ta sanar, sun hada da fitattun jarumai irin su mawaka Nina Chuba da Clueso, da darektan cibiyar German – Turkey Fatih Akin, da fitaccen mai shirya fina-finai a Jamus wanda ya lashe lambar yabo ta Golden Globe, Ari Folman, da kuma fitacciyar jarumar sinima ta Jamus Sandra Hüller.
Kungiyar ta kuma soki lamirin firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu kan aniyar mamaye yankin zirin Gaza gaba daya, tare da yin kira ga shugaba Friedrich Merz da ya dauki matakin gaggawa kan wannan batu.
Wannan ya biyo bayan wata budaddiyar wasika da wasu fitattun Jamusawa fiye da 200 suka fitar ne a ranar Alhamis din da ta gabata, wadanda suka bukaci a kawo karshen baiwa Isra’ila makamai tare da yin kira da a kakaba mata takunkumi, saboda hare-haren kisan kiyashin da take aiwatarwa a zirin Gaza.