Jami’in Yemen Ya Ce: Samuwar ‘Yan Sahayoniyya A Yankin Gabas Ta Tsakiya Babbar Matsala Ce Ga Yankin 

Babban jami’in kasar Yemen kuma kakakin kungiyar Ansarullhi ta Mabiya Huthi ya jaddada cewa: Ba ​​za a taba samun zaman lafiya na hakika a yankin

Babban jami’in kasar Yemen kuma kakakin kungiyar Ansarullhi ta Mabiya Huthi ya jaddada cewa: Ba ​​za a taba samun zaman lafiya na hakika a yankin Gabas ta Tsakiya ba sai an kawar da ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya

Shugaban tawagar masu shiga tsakani na kasa na kasar Yemen, kuma kakakin kungiyar Ansarullahi ta Mabiya Huthi, Mohammed Abdul Salam, ya jinjinawa al’ummar Gaza kan irin tsayin dakan da suka yi wajen tunkarar wuce gona da irin na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai jaddada cewa batun Falastinu shi ne abu na farko a cikin zukatan al’ummu, kuma ba za a taba  samun zaman lafiya na hakika a yankin ba, sai an samu nasarar kawar da wannan haramtacciyar kasar ta Isra’ila da kasashen yammacin turai da Amurka suka dasa ta da karfi tsiya domin cimma munanan manufofinsu a kan al’ummar Falasdinu da sauran al’ummun yankin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Abdul Salam ya bayyana jin dadinsa kan yadda al’ummar kasar Yemen masu kauna da kuma sojojin su suka iya sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na tallafa wa Gaza tare da gudanar da zanga-zangar miliyan mutane a kowane mako da kuma gudanar da ayyukan soji masu tasiri kan makiya tun daga farkon bullar harin daukan fans ana AmbaliyarAl-Aqsa har zuwa lokacin da aka sanar da tsagaita bude wuta a Gaza.

Abdul Salam ya ce: “Duk da ci gaba da killace kasarsu, da yadda aka raunata al’ummar Yemen sakamakon hare-haren wuce gona da iri da aka din ga kai wa kan su a baya da kuma mawuyacin halin da ake ciki na tattalin arziki a kasar, amma hakan bai sa su yi kasa a gwiwa ba, sai dai kara samun kwarin gwiwa tare da karfin zuciya kan tallafawa Gaza, da yake nauyi ne na addini da na jin kai wanda dukkanin al’ummar kasar ke da alhakinsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments