Jami’in Iran Ya Sanar Da Sabon Shugaban Amurka Cewa: Manufar Iran Ita Ce Neman Hakkokinta

Mamba a Majalisar fayyace masalahar tsarin Musulunci ta kasar Iran ya fadawa Trump cewa: Manufar al’ummar Iran ita ce cimma hakkokinsu tabbatattu ba tare ganin

Mamba a Majalisar fayyace masalahar tsarin Musulunci ta kasar Iran ya fadawa Trump cewa: Manufar al’ummar Iran ita ce cimma hakkokinsu tabbatattu ba tare ganin an tauyaye musu ba

Mamba a majalisar fayyace masalahar tsarin Musulunci a kasar Iran Mohsen Reza’ei ya bayyana cewa: Aniyar al’ummar Iran ita ce neman kai wa ga hakkokinsu domin ganin sun tabbata kuma ba za su taba girgiza kan haka ba.

A cikin wani sakon da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X, Reza’ei ya kara da cewa: Dole ne Donald Trump ya yi nadamar kuskuren da ya yi a baya shi da sauran shugabannin Amurka kan munanan matakan da  suka dauka kan kasar Iran.

Ya ci gaba da cewa: Manufar al’ummar Iran ita ce ganin an bi musu hakkinsu tare da tabbatar da su kuma babu abin da zai girgiza su kan kyakkyawar aniyarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments