Daraktan ofishin yada labarai na gwamnatin Falasdinu a Zirin Gaza Isma’il Al-Thawabitah, ya jaddada cewa: Hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kai kan yankin ya yi sanadin mutuwar shahidai sama da dubu 60 tsakanin kisan gilla da wadanda suka bace, tare da rusa wasu muhimman sassa fiye da 15 a Zirin na Gaza, yana mai cewa kai tsaye, hasarar farko da aka yi wa wadannan sassa a sakamakon yakin kisan kare dangi ya haura kudi dala biliyan 38.
A wata hira ta musamman da tashar talabijin ta Al-Alam ta kasar Iran ta yi da Al-Thawabita ya kara da cewa: Wannan yakin da ya dauki tsawon kwanaki 470 ya kunshi kashe-kashe da kisan kare dangi da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi, tare da rusa wasu muhimman sassa fiye da 15 a Zirin Gaza, kuma na farko sun shafi cibiyoyin rayuwar al’umma kai tsaye sakamakon hasarar yakin kisan gillar ya haura dala biliyan 38, baya ga gudun hijirar da haramtacciyar kasar Isra’ila ta tilasta wa falasdinawa yi, wanda hakan laifi ne na cin zarafin bil’adama kamar yadda dokokin kasa da kasa, da dokokin jin kai na kasa da kasa, da duk wasu dokoki suka tabbtar da su.