Jami’ar Colombiya Ta Birnin New York A Amurka Ta Dakatar Da Karatun Daliban Jami’ar Fiye Da 65

Hukumomi a Jami’ar Colombia dake birnin NewYork na kasar Amurka sun bada sanarwan cewa, sun dakatar da karatun daliban jami’ar fiye da 65 saboda shiga

Hukumomi a Jami’ar Colombia dake birnin NewYork na kasar Amurka sun bada sanarwan cewa, sun dakatar da karatun daliban jami’ar fiye da 65 saboda shiga cikin zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kusa da babban dakin ajiyar littafai ko karatu a Jami’ar a ranar Laraban da ta gabata.

Tashar talabijin ta Press tv a nan Tehran ta nakalto kakakin Jami’ar a jiya Jumma’a na cewa a ranar Laraba yansandan NewYork sun kama talibai kimani 80 inda suke tsare da su, a halin yanzu suke kuma ci gaba da gudanar da bincike a kansu. Amma duk da haka an dakatar da karatun wasu daga cikinsu zuwa wani lokaci nan gaba.

Labarin ya kara da cewa akwai wasu karin mutane 33 wadanda Jami’ar ta dakatar saboda hannun a cikin zanga-zangar goyon bayan Falasdinawar.

Labarin ya bayyana cewa hotunan bidiyo na tsaro a dakin karatu na Jami’ar sun nuna daliban suna shiga dakin sannan jami’an tsaro suna binsu suna kamawa, sannan wasu daga cikinsu na sanye da ‘Keffiyeh’ wani kelle wanada yake nuna alamar Falasdinawa.

Jami’o’ii da dama a Amurka suna gudanar da irin wannan zanga-zangar, don nuan rashin amincewarsu da kissan kiyashen da HKI take yi a gaza tun shekara ta 2023 ya zuwa yanzu, da kuma tallafa mata wanda gwamnatin kasar ta Amurka take yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments