Tsohuwar jami’ar leken asiri a rundunar sojin Amurka Josephine Guilbault ta ce: Majalisar Dokokin Amurka na da hannu dumu-dumu a kisan kiyashin da ake yi a Gaza ta hanyar goyon bayan da Amurka ke ba haramtacciyar kasar Isra’ila musamman na aike mata da muggan makamai da karfafa ta da kudade.
Wannan dai ya zo ne a cikin jawabin da kwamitin kula da harkokin soji ya gudanar a Majalisar wakilan Amurka a jiya Alhamis, inda Guilbault ta nuna rashin gamsuwarta da manufofin gwamnatin Amurka da Majalisar dokokin kasar game da gwamnatin mamayar Isra’ila.
A yayin zaman, Guilbault ta tashi tsaye ta yi wa ‘yan majalisar jawabi a cikin kakin soja, tana mai cewa: Majalisar dokokin Amurka abokiyar kawance ce a wannan kisan kare dangi da ke faruwa a Gaza, kuma ci gaba da aika biliyoyin daloli zuwa ga gwamnatin Isra’ila bai dace ba. Guilbault ta jaddada cewa: A matsayinta ta jami’ar da ta yi aiki na tsawon shekaru 17 a cibiyar leken asiri, ita shaida ce kan yadda mahukuntan Amurka suke rusa kimar Amurka da tsaron kasarta.
Ta ce: Haramtacciyar kasar Isra’ila tana kona yara da ransu a Gaza yau fiye da tsawon shekara guda, lamarin da ya zubar da zubar da daraja da kimar Amurka a idon duniya.