Yansanda a kasar Amurka suna ci gaba da dirar mikiya kan daliban jami’o’ii a kasar wadanda suke goyon bayan kasar Falasdinu. Tun ranar 17 ga watan Afirilun da ya gabata ne daliban Jami’ar Colombia a birnin NewYork na kasar Amurka suka fara zaman dirshen da zanga zanga a cikin harabar jami’ar, inda suke nuna goyon bayansu ga kasar Falasdinu, kuma suke kira ga gwamnatin shugaba Biden ta dakatar da bawa gwamnatin HKI makamai ta kuma kawo karshen yakin da ake a gaza.
Daga nan boren daliban jami’o’ii ya fara yaduwa zuwa sauran jami’o’iin kasar wadanda a halin yanzi adadinsu ya fi 100. Banda haka, wannan goyon bayan da kuma bukatar a dakatar da kissan kiyashi a gaza ya yadu har zuwa jami’o’in kasashen Turai da Canada da wasu kasashe.
Majiyar kamfanin dillancin labaran IRIB NEWS tun ranar 17 ga watan Afrilu zuwa yanzun jami’an yansanda a kasar Amurka ta kama daliban jami’o’ii kimai 2000 sun tsare. Labarin ya kara da cewa a jami’ar “The New School University na birnin New York’ jami’an yansanda sun kama dalibai 43. Sannan a jami’ar Cicago daliban sun ci gaba da zaman dirshen a wani wuri a cikin jami’ar duk tare da kawanyan da jami’an yansanda suka yiwa Jami’ar. Sai kuma jami’ar Princeton yansanda sun kama daliban jami’a 15 masu zaman dirshen saboda goyon bayan Falasdinawa. A Jami’at Pontland sun kama daliban jami’a 12, sai Jami’ar NewYork inda suka kama dalibai 13. Wata majiya ta bayyana cewa yawan daliban jami’o’in da yansanda suka kama a Amurka saboda goyon bayan Falasdinawa sun fi 2,200 amma duk da haka daliban sauran jami’o’in suna ci gaba da zaman dirshen da kuma bukatar a dakatar da yaki a gaza.
Makamai Masu Linzami Sun Fada Kan Sansanin Sojojin Amurka A Gabacin Kasar Siriya
Makamai masu linzami sun fada kan sansanin sojojin Amurka dake ‘yankin umari’ mai arzikin man fetur a gabacin kasar Siriya.
Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bayyana cewa makamai masu linzami akalla 7 ne suka fada kan sansanin sojojin na Amurka a kusa da rijiyoyin hakar man fetur na (Umari) a cikin lardin Dair-zur na gabacin kasar Siriya a jiya Jumma’a.