Jami’an Tsaron Iran Sun Kama Wani Dan Ta’adda Tare Da Jin Makirce-Makircen Kungiyarsu

Wani dan kungiyar ta’addanci da aka kama a shiyar kudu maso gabashin kasar Iran ya yi ikirari kan irin zagon kasa da suke kitsa kan

Wani dan kungiyar ta’addanci da aka kama a shiyar kudu maso gabashin kasar Iran ya yi ikirari kan irin zagon kasa da suke kitsa kan al’ummar Iran

Sakamakon habakar hare-haren ta’addancin baya-bayan nan a lardin Sistan da Baluchestan da ke gabashin kasar Iran, jami’an tsaron kasar sun kama wani dan kungiyar ta’addanci ta “Jaysh al-Adil”.

Dan ta’addan da aka kama, yana daya daga cikin wadanda suka kai harin ta’addanci kan masu shirya bikin nuna farin ciki (wanda ake gudanarwa duk shekara domin taimaka wa dalibai mabukata a daf lokacin fara karatun shekara a duk fadin kasar) a garin Bint da ke kudancin lardin Sistan da Baluchestan, inda ya yi ikirari mai ban tsoro bayan binciken da aka gudanar kansa.

Wannan dan ta’adda mai shekaru 20 a duniya ya ce: Wani mai suna “Abdul Rahman Malik Ra’isi,” wanda aka fi sani da “Ajmal” ko “Jassim Sarzabi,” shi ne ke kula da shugabancin kungiyarsu a lardinsu.

Wannan dan ta’addan ya kara da cewa: Kungiyarsu ta dauka wa kanta cewa a duk lokacin da take fuskantar matsin lamban tattalin arziki, za ta din ga yin garkuwa da mutane don karbar kudaden fansa da nufin samun ci gaba da gudanar da harkokinta, kuma yana daga cikin masu dasa nakiyoyi a gefen hanyar shigewar jami’an tsaron kan iyaka da motocin jami’an tsaron cikin gida tare da tarwatsa su.

Ya ci gaba da cewa: Sauran aikin da kungiyar ta ba su akwai mayar da hanyar zirga-zirgar Chabahar maras tsaro, wadda ake ganin ta zama wata muhimmiyar hanyar zirga-zirgar ababan hawa, inda kungiyar take tayar da bama-bamai da gudanar da ayyukan zagon kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments