Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Watsi Da Zarge-Zargen Kasar Amurka Ke Yi Kanta  

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta aike da sako ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya kan zargin Amurka da kai harin wuce gona da iri kan

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta aike da sako ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya kan zargin Amurka da kai harin wuce gona da iri kan kasar Yemen

A cikin wata wasika da jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran kuma wakilinta na din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’id Irawani ya aike wa shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana zargin da Amurka ke yi kan kasar Yemen da cewa ba shi da tushe balle makama, inda ya ce: Iran a ko da yaushe tana jaddada yadda za a warware rikicin Yemen ta hanyar lumana karkashin salon diflomasiyya.

Jakadan na Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya kuma jaddadawa shugaban rikon kwarya na kwamitin sulhu da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a cikin wasikarsa cewa: Ina so ya mayar da martani ga daya daga cikin zarge-zargen da jakadan Amurka ya yi ne kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kan tubalin kiyayya a lokacin bude zaman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan halin da ake ciki a kasar Yemen, wanda aka gudanar a ranar 13 ga watan Yunin wannan shekara ta 2024 a karkashin tsarin ajandar halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.

Irawani yana mai bayyana cewa: Abin takaici, wakilin Amurka, saboda tubalin tsarin da kasarsa ta saba tafiya a kai, ya yi amfani da dandalin Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya wajen zargin wasu kasashe masu cin gashin kansu. Yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da wadannan zarge-zargen da ba su da tushe balle makama. Tana mai jaddada bukatar ta kuduri aniyar bin kudurorin kwamitin sulhun da suka dace dangane da halin da ake ciki a kasar Yemen kuma ba ta shiga cikin ayyukan da suka saba wa wadannan kudurori.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments