Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya soki mummunar rawar da Faransa ke takawa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya soki kasar Faransa saboda abin da ya bayyana a matsayin gurgunta rawar da take takawa a kokarin diflomasiyya kan matsayin Shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya.
A wani rubutu da ya yi a dandalin X, kakakin ya yi tsokaci kan zargin na Faransa, yana mai cewa: Ikirarin da ministan harkokin wajen Faransa ya yi na cewa Iran na daf da kera makamin nukiliya, da’awa ce ta karya kuma marar tushe.
Ya kara da cewa: Wadannan kalamai na karya, tare da barazanar sake kakabawa Iran takunkumi, suna kara karfafa ra’ayin cewa matsayar Faransa na rikidewa zuwa wani matsayi na barna.
Ya ci gaba da cewa: Irin wannan tsarin ba zai karawa Faransa kwarin gwiwa ko matsayinta a Turai ko duniya ba.