Jakadan kasar Siriya a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Wasu kasashen yanki da na duniya suna amfani da ta’addanci don cimma manufofinsu
Jakadan kasar Siriya a Majalisar Dinkin Duniya Qusay al-Dahhak ya bayyana cewa: Girman hare-haren da ‘yan ta’adda suke kaddamarwa a cikin kasar Siriya yana nuni da irin gagarumin goyon bayan da suke samu daga bangarorin yankin da na kasa da kasa da nufin aiwatar da manufofin kasashen waje bayan janyo cikas ga zaman lafiyar kasar ta Siriya.
A jawabinsa a yayin zaman kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, Jakadan kasar Siriya ya bayyana cewa: Harin ta’addancin da aka kai a birnin Aleppo ya zo ne a daidai lokacin kwararar ‘yan ta’adda a kan iyakar arewacin kasar da kuma karin taimakon da ake ba su daga kasashen waje da suka hada da kayan yaki, manyan makamai, motoci, jirage marasa matuka ciki na zamani, kayayyakin fasahar sadarwa, da kuma tabbatar da layukan samar da kayan aikin soja da na kayan aiki.
Ya kuma jaddada cewa: Ba za a iya kai harin ta’addancin da aka kai a arewacin kasar Siriya ba, ba tare da hadin gwiwa tsakanin kasar Turkiyya da haramtacciyar kasar Isra’ila ba, lamarin da ya share fagen da haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kasar Siriya.
Yana mai jaddada cewa: Hare-haren ta’addanci ya tilastawa dubban iyalai a birnin Aleppo tserewa zuwa yankunan da suke karkashin ikon gwamnatin Siriya, yayin da wadanda suka makale a cikin birnin ke fuskantar mawuyacin hali na jin kai da hare-haren wuce gona da iri daga kungiyoyin ‘yan ta’adda.