Jakadan kasar Rasha a hukumar IAEA mai kula da al-amuran makamashin nukliya ta duniya ya bayyana cewa hukumar IAEA ta zama mai amshin shatan kasashen yamma musamman Amurka, maimakon ta nuna adalci da rashin nuna bambamci a matsayinta na kungiya ta kasa da kasa.
Mikhail Ulyunuv jakadan kasar Rasha a Vieanna ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da jaridar kasar rasha mai suna Kommersant,a jiya Lahadi.
Ya kuma kara a cewa babu wanda yake da labari ko masnani kan cewa Iran tana da wani shiri na tashe makamashin Uranium a karkashin duwatsun Kolang na kasar Iran. Amma gwamnatin Amurka ta fito a fili tana maganar cewa ta gano cewa Iran tana tace makamashin Uranium a karkashin wannan dotsen kuma ba tare da wani bincike ba, hukumar IAEA ta dauke tana kuma bukatar wai Iran ta yi bayani a kan wannan shirin.
Amurka ta sanya hare haren ta na gaba a kan Iran zai maida hankali ne kan wadan nan duwatsu da kuma shirin JMI na makamashin nukliyar da ba’a tabbatar da dake karkashin duwatson. Ilyanuf ya bayyana cewa, Iran bata taba bada rahoton wannan shirin ba, haka ma hukumar ta IAEA bata bata bata rahoton tana da masanin kan shirin ba.