Rahotanni sun bayyana cewa Jagororin kungiyoyin gwagwarmaya da suka ziyarci ofishin jakadancin Iran dake birnin Damaskas na kasar siriya sun taya iran murna game da Nasarar da ta samu na kai harin gargadi na alkwarin gaskiya da ta kai wa Isra’ila, tare da bayyana harin a matsayin hakkinta ne da doka ta bata,
Ko a kwanakin baya ma shuwagabannin kungiyoyin yan gwagwarmayar falasdinu sun kai ziyara ofishin jakadancin Iran dake birnin Berut na kasar labanon kuma sun mika sakon taya murna game da irin nasarar da Iran ta samu na kai harin jan kunne na Alkawarin gaskiya, Harin na gargadi na alkwarin gaskiya da iran ta kai baya ga rusa wuraren soji na Isra’ila da suka hada da sansanin leken asirinta dake yankin Jabal sheikh , da kuma sansanin soji sama na Navotim kuma ya haifar da mummunar asara ga dakarun sojin saman kasar .