Chuck Schumer: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela

Jagoran ‘Yan Jam’iyyar Democrat na Majalisar Dattawa Chuck Schumer ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da shirya  yaƙi a ɓoye a kan kasar Venezuela, yana

Jagoran ‘Yan Jam’iyyar Democrat na Majalisar Dattawa Chuck Schumer ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da shirya  yaƙi a ɓoye a kan kasar Venezuela, yana mai jaddada cewa ikon ayyana yaƙi ya rataya ne kawai a kan Majalisa, kuma dan majalisar ya bayyana cewa zai  gabatar da kuduri  don hana tura sojojin Amurka yaki a Venezuela.

Schumer ya tabbatar da cewa Trump ba shi da ikon aika sojojin Amurka zuwa yaƙi ba tare da izinin Majalisa ba, yana mai bayyana  cewa wannan ikon an keɓe shi ne ga Majalisa kaɗai.

A cikin wata sanarwa, Schumer ya zargi Trump da shirin yaƙi a ɓoye da Venezuela, yana mai gargadin cewa Majalisa za ta ɗauki mataki nan take don gabatar da kuduri zai hana hana tura sojojin Amurka zuwa wannan yaki da yake Shirin kaddamarwa.

Schumer ya ce mutanen Amurka ba sa son wani yaƙi da ba a san karshensa ba,  ya ƙara da cewa duk wani mataki mai ƙarfi a kan Venezuela ba tare da amincewar majalisa ba zai zama babban kure da kuma sab awa doka.

A wani labarin kuma, Schumer ya bayyana cewa ya sami barazana ta imel,  daga abin da ya kira “MAGA” ko kuma (Make America Great Again) wato gungun da ke mara baya ido rufe ga siyasar Trump, kuma ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro a New York sun sanar da shi barazanar da aka yi lokuta daban-daban na dana bam a ofisoshinsa.

A ranar Asabar da ta gabata, shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa za a rufe sararin samaniyar Venezuela da yankin da ke kewaye da ita gaba daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments