Search
Close this search box.

Jagoran Musulunci Na Iran Ya Bayyana Sabuwar Shekara A Matsayin Ta Bunkasa Kere-kere Da Hadin Guiwa Da Alumma

A cikin sakon taya murnar  shiga sabuwar shekara ta 1403 ta hijira shamsiyya da Jagoran juyin musulunci na kasar Iran Ayatullah Imam Khamna’I ya yi 

A cikin sakon taya murnar  shiga sabuwar shekara ta 1403 ta hijira shamsiyya da Jagoran juyin musulunci na kasar Iran Ayatullah Imam Khamna’I ya yi  a yau laraba 20 ga watan maris a sanyawa sabuwar shekarar sunan shekarar bunkasa kere-kere da hadin guiwar Alumma,

Yace zan so na aike da sakon taya murna ga dukkan alummar kasar iran  na zagayowar sabuwar shekarar hijira Shamasiya wadda ta zo daidai da lokacin Azumin watan ramadana mai alfarma wanda yake dausayin zukata da kuma maasanawiya, musamman ga iyalan wadanda suka jikkata a fagen yaki da sauran alummomin duniya da suke gudanar da bukin sabuwar shekara na Nooruz,

Haka zalika jagoran ya kara da cewa ina kara jinjina ga dukkan shahidanmu  da kuma shugaban shahidai  wanda ya bude wannan hanyar ga Alummar iran,  yace yana fatan Alummar iran za su ci gajiyar wadandan dausayin guda biyu  na raya zukata da kuma karfafa kusanci da mahalicci.

Da yake bayani game da batun bunkasa kasa kuwa ya nuna cewa kere-kere yana daga cikin muhimmanbatu wnana yasa ma  a wannan shekarar na sake mayar da hankali a kansa a wanna shekarar, ina da cike da fata cikin hardar ubangiji  zamu fuskanci ci gaba sosai a bangaren kere-kere , sai dai nayi imani cewa ci gaban kere-kere ba zai samu ba ta re da yin hadin guiwa da Alumma ba, da kuma damwa da su a wannan bangaren  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments