Jagora: Yahudawan Sahayoniyya Sune Mafi Kyamar Al’umma A Duniya Saboda Muggan Halayensu

shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin harshen Yahudanci ya bayyana cewa: ‘Yan sahayoniyya sune wadanda aka fi kyamata a duniya Shafin Jagoran juyin

shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin harshen Yahudanci ya bayyana cewa: ‘Yan sahayoniyya sune wadanda aka fi kyamata a duniya

Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci na yaren yahudanci a shafin sada zumunta na X ya rubuta cewa: Makiyar al’ummar Iran na kan gaba a yau ita ce, gwamnatin ‘yan sahayoniyya wacce ita ce mafi kyamata a tsakanin al’ummar duniya.

Shafin yanar gizo na KHAMENEI.IR na yaren yahudanci ya wallafa wani kaso na jawabin Jagoran a jiya litinin a wajen taron juyayin shahadar Imam Ali dan Musa al-Rida Jagoran shiriya na Iyalan gidan Manzon Allah {s.aw}.

Sanarwar ta kara da cewa: “Makiyar al’ummar Iran a yau, ita ce gwamnatin ‘yan sahayoniyya, wacce duniya ta fi kyama a duniya. Mutane suna kyamatar gwamnatin ‘yan sahayoniyya, har ma gwamnatocin kasashen duniya suna la’antarta.”

A safiyar ranar Lahadi, a daidai lokacin da ake tunawa domin nuna alhinin shahadar Imam Ali dan Musa al-Rida (AS), a lokacin da yake ganawa da dubban al’ummar kasar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin yadda mazhabar Ahlul-baiti (AS) ta bambanta da kuma ci gaba da yada al’amarin Ashura da kuma falsafar yunkurin Imam Husaini (AS) a duniyar musulmi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted